Daga Kamal Yakubu Ali
Al’amura sun fara rinchabewa a Majalisar Dokokin Jihar Kano, domin kuwa an fara shirin tsige Shugaban Majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, da Mataimakinsa, Zubairu Hamza Massu.
Jaridar Politics Digest ta rawaito cewa shirin yana da nasaba da goyon bayan da Shugaban Majalisar da Mataimakinsa suke yiwa tsohon kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum na takarar gwamna da yake.
An yi zargin cewa kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Murtala Sule Garo, yana tare da yunkurin ‘yan majalisar na tsige Shugaban Majalisar da Mataimakinsa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdul Madari, mai wakiltar mazabar Warawa, da tsohon kakakin majalisar, Abdulaziz Gafasa, suma suna da hannu dumu-dumu a shirin tsigewar bisa umarnin Garo.
Shirin tsigewar ya biyo bayan babban taron jam’iyyar APC na Kano ta Kudu da ya gudana a Rano.
Duka Cidari da Mataimakinsa sun kasance masu goyon bayan ga Kabiru Rurum lokacin da yake Shugaban Majalisar.
Murtala Garo na daya daga cikin manyan makusantan gwamna kuma na kusa da shi. Jama’a da dama na yi masa kallon wanda zai tsaya takarar gwamna saboda irin goyon bayan da yake samu daga uwargidan Gwamnan Hafsat Ganduje.
A baya-bayan nan dai ana kallon Sanata Barau Jibrin a matsayin wanda ya fi kowa adawa da Garo amma sai ga shi Rurum ya fito daga sansanin gwamnan. Hakan ya ba shi karfin gwaiwa fiye da Barau da ke cikin bangaren G7 na APC a jihar kano.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya da Bunkure, Rurum, yana samun gagarumin goyon baya daga ‘yan majalisar jiha a takararsa ta gwamna.
A kwanakin baya ne wasu masu ruwa da tsaki daga Kano ta Kudu suka amince da Rurum a matsayin Dan takarar su na gwamnan jihar Kano, Ado Doguwa, kakakin majalisar wakilai da kuma Sanata Kawu Sumaila, dukkansu ’yan Gudunmawar Kano ta Kudu ne.
An yi ta tayar da jijiyar wuya da mutanen shiyyar suka yi na karbar mulki daga hannun Ganduje.
A cewar masu ruwa da tsakin, shiyyar har yanzu ba ta samar da gwamna ko mataimakinsa ba tun 1993, don haka suke goyon bayan Rurum.