Sojojin Rasha sun doshi Kyiv babban birnin Ukraine

Date:

 

Sojojin Ukraine na ci gaba da ƙarfafa tsaron Kyiv yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da ƙoƙarin kutsawa cikin babban birnin kasar.

Sojoji sun yi ta tona ramuka tare da toshe hanyoyi ta amfani da tankokin yaki.

Hukumomin ƙasar sun ce ana ci gaba da luguden wuta a biranen uku da ke arewa maso yammacin Kyiv — Bucha, Hostomel da Irpin.

Ana ci gaba da gwabza kazamin faɗa a yankin. Dakarun Rasha sun harba rokoki kan fararen hula a Irpin a lokacin da suke ƙoƙarinrin tserewa, inda suka kashe wata uwa da yara biyu tare da raunata mahaifinsu.

An kuma tarwatsa wata gada ta wuccin gadi da mutane ke ratsa kogi domin tserewa daga ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta ilimi: Shugaban Karamar hukumar Ungoggo ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwar

Daga Shehu Usaini Getso Shugaban karamar hukumar Ungoggo Alhaji Tijjani...

Karyewar gada ya jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali a Rano, Sun nemi Agajin Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Al’ummar garuruwan Kazaurawa/Unguwar Ganji da ke...

Rashin tsaro: Tinubu na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na...

Ban ce filin makarantar Bechi nawa ba ne, Kuma zan taimaka wajen gini Makarantar – Alh. Sagir Jaen

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Biyo bayan koken da al'ummar garin...