SHIRIN LULU DA ANDALU…LABARI NE DA YA FARU A GASKE…
Rubutawa Shariff Aminu Ahlan Fassara Yaya Muhammad.
Masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood ta zarce tunanin masu tunani, musamman wanda yasan yadda masana’antar ta faro sama da shekaru talatin baya zuwa yanzu. Nayi imanin wani zai gaskata abinda nake fada cewar an samu cigaba kwarai da gaske wanda hakan yasa duniya tasan da zaman masana’antar a matsayin masana’antar dake bunkasa sakamakon irin nagartattun fina-finan da ake samarwa duk kuwa da kalubalan kudi sakamakon karancin samun tallafi ko zuba jari daga bangaran gwamnati ko da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin film na Duniya.
Zuwa yanzu masanaantar shirya fina- finan Hausa ta dauki wata sabuwar turba ta cigaba, Wanda nan gaba kadan duniya zata Kara gamsuwa da aiyukan Kannywood Wanda hakan zaisa masana’antar fara karbar manyan lambobin yabo a mataki na Duniya, sakamakon fara daukar wani ingantacce kuma nagartaccen sabon shirin film mai dogon zango maisuna “Lulu da Andalu” Wanda duk kanin abinda labarin ya kunsa abu ne da ya faru a zahiri.
MANSA MUSA wani shaharerren mai dukiya ne dan kasar MALI wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taba zama mutumin da babu wanda ya kaishi tarin dukiya a fadin duniya, yayi mulkinsa a matsayin MANSA na MALI tsakanin shekara ta 1312 sannan kuma ya rasu a shekara ta 1337.
Sai kuma kwatsam a wannan zamanin namu na shekara 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shi ne ya gano inda dukiyar MANSA MUSA take domin ya mallaketa, sai dai kafin gano inda dukiyar MANSA MUSA take dole sai an taso da wasu hatsabiban Aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga wani dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata suna shekar kayansu.
Haka kuma shirin film din zai nuna yadda dangantaka da mu’amular rayuwa ke gudana tsakanin bil’adama da ‘Jinnu” ta yadda mutane da aljanu za suyi aiki tare wajan gano maboyar da aka killace tarin dukiyar, inda bil’adama da jinnu za suyi amfani da tsafi wajan gudanar da aikinsu. Ko ta Yaya hakan zai yuwu?? Wannan na daga cikin tarin tambayoyin da mutane keyi.
Domin tabbatar da yuwar wannan aikin film, mashiryin Shirin film din Lulu da Andalu ya dauki kwararrun masana aikin shirya film da jarumai maza da mata domin tabbatar da ganin wannan gagarimin aiki ya zama gaskiya, Wanda zai gamsar da duniya makallata fina- finai a fadin Duniya.
Wannan wani abun yabawa ne bisa bijiro da wannan aiki duk kuwa da yanzu haka ana kan gudanar da aikin ne, shirin film din da kaso tamanin 80% cikin dari sabbin abubuwa ne a cikinsa Wanda ke bukatar kwararru wajan aiwatar da shi, wannan ce tasa duk kanin jaruman dake taka rawa a cikin film din saida aka basu kwaryar kwaryan horo domin kara sanin makamar aiki yadda ya kamata.
Daga karshe dai Muna fatan ganin Gawurtaccen film daga masana’antar shirya fina-finan Kannywood wanda zai gamsar da masu kallo na fadin Duniya, Wanda hakan zai janyo tafka muhawara a tsakanin jama’a.
Saboda haka mu jira fitowar wannan kayataccen shiri da zarar an Kamala aikinshi. Jin jina ga duk kanin masu ruwa da tsaki na Shirin LULU DA ANDALU.