Inganta tsaro:An baiwa Matasa horon yadda zasu rika taimakawa Jami’an tsaro da bayanan Sirri a kano

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi

Wata kungiya mai rajin taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri dake Jihar Kano tayi bikin yaye dalibai da suka samu hora  akan hanyoyin da za subi domin taimakawa harkokin tsaro musamman wajan daqile ayyukan batagari ta kowanne irin yanayi.

Yayin da yake gabatar da Jawabi a wajen taron Musbahu Aminu yahaya Wanda Kuma gudane daga cikin shugabannin kungiyar ya bayyana cewa sun shirya taron horaswar ne domin Magance Matsalolin tsaro da Suka addabi al’umma.

Yace an Shirya horon ne ga maza da mata domin kowanne daga cikin su akai irin gudunmawar da zai bayar domin cigaban al’ummarsu.

“An saka mata a cikin wannan horaswarne domin su ke shiga gidajen biki da suna Kuma zasu Sami bayanai sosai Waɗanda zasu taimaka don Inganta tsaro “. Inji Musbahu

Ya bayyana cewa ta hakane zasu rika samun bayanan sirri domin ankarar da hukumomin da Abun ya shafa domin daukan matakin da Suka dace kafin lamarin ya tu’azzara.

Wasu daga cikin Waɗanda suka sami wannan horan sun baiyana cewa hakika sun ilmantu sosai da horon tare Kuma da bada tabbacin za suyi aiki tukuru danganin anfudda jaki daga duma.

Taro dai ya samu halartar manya manyan alqalai da mafiya yawa daga masu unguwannin kewayen cikin gari da kuma manyan jami’an yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...