Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hafsat Idris, ta karyata rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa ta auri dan tsohon shugaban kasar Najeriya.
Kadaura24 ta rawaito Hafsat, wacce da farko ta ki cewa komai kan Kan batun auren nata, daga baya ta bayyana a shafinta na Instagram cewa mijinta ba dan tsohon shugaban kasa bane.
A yayin da take tabbatar da labarin auren nata, jarumar da aka fi sani da Ɓarauniya ta bayyana cewa mijin nata ba shi da wata alaka ta kusa ko ta nesa da gidan tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Sani Abacha.
A cewar wata majiya mafi kusa da ita, jarumar an daura aurenta ne da wani Mukthar Hassan Hadi a ranar 26 ga Fabrairu, 2022.