Kakakin fadar gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov, ya ce umarnin da Shugaba Putin ya bayar ranar Lahadi ga dakarun ƙasar na su kasance cikin shirin amfani da makaman ƙasar ciki har da na Nukiliya martani ne ga Sakatariyar harkokin Wajen Birtaniya Liz Truss.
Mista Peskov ya ce akwai kalamai na rashin kamun kai waɗanda ba za a lamunta ba, da ke fitowa daga bakin wakilai daban-daban na ƙasashen Turai game da fito-na-fito tsakanin NATO da Rasha, ciki har da wanda ministar harkokin wajen Birtaniyar ta yi.
Ministan tsaro na Birtaniyar, Ben Wallace, ya ce Birtaniya ta kalli matsayin na Rasha a kan makaman kare-dangi, kuma ta lura cewa babu wani sauyi na a zo a gani a kai.
Ya ce Mista Putin, yana son ya nuna karfin Rasha ne, ta hanyar ambato shirin ko ta kwana na amfani da makaman nukiliyar na kasarsa.