Kotu ta yanke wa wani kurma hukunci sakamakon sayar da wiwi a Kano

Date:

 

Kotun Majistare mai lamba 47, ƙarƙashin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, a jiya Litinin ta yanke wa wani kurma hukunci har kashi uku.

Tun da fari dai, an gurfanar da kurman ne bisa tuhumar haɗa kai da uzzurawa al’umma wajen haɗin gwiwa da wasu ɓatagari su na siyar da tabar wiwi.

Ko da jami’in kotun, Auwal Yakubu Abdullahi ya karanto masa tuhumar, nan take ya amsa laifin sa, inda hakan ya sa kotu ta yanke masa wannan hukuncin.

Daily Nigerian ta rawaito Hukuncin farko, an yanke masa wata 6 ko tarar naira dubu 10, sai kuma ɗaurin shekara 1 ko tarar naira dubu 30, sannan kuma sai ɗaurin wata uku ko tarar naira dubu 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...