Tallafawa Talakawa: Ana zargin Gwamnan Zamfara da karkatar da Sama da Naira Miliyan 100 duk wata

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru
Mai kwarmaton nan na jihar Zamfara, Aminu Umar (Game-Game) ya sake tuna Zargin wata badakala a gwamnatin jihar Zamfara inda ake karkatar da Naira miliyan dari da saba’in da shida duk wata.
Shugaban Ma’aikatan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya Sanyawa hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.
 Aminu Umar wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Ofishin  mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau ya ce ana ciro naira miliyan 176,000,000.00 daga asusun kananan hukumomi 14 na jihar da sunan shirin bada tallafi ga al’umma a Jihar Zamfara Wato Z-SIP wanda aka tsara domin rage radadin talauci a jihar.
 Shugaban Ma’aikatan ya bayyana cewa, gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle shi ne mai kula da duk wani asusun gwamnati a jihar Kuma shi ne Mai bada Umarnin shiga ko Fitar kudi a asusun jiha, kuma yana ganin alamar duk wata hada-hadar kudin Gwamnatin jihar.
 A cewarsa, shirin na Z-SIP ya fara ne a cikin watan Fabrairu, 2020 inda ake sa ran dukkan wadanda za su ci gajiyar shirin za su rika karbar Naira Dubu Goma (N10,000) duk wata kuma sun karbi alawus din na karshe tun watan Nuwamba, 2020.  amma duk wata ana cire Naira 176,000,000.00 daga asusun kananan hukumomi .
 Aminu Game-Game wanda ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin Gwamna Bello Mohammed Matawalle da ya bayyana yadda take kashe kudaden, ya ce Naira Miliyan Saba’in da Shida ne kawai ake biyan wadanda za su ci gajiyar tallafin yayin da ake karkatar da sauran Naira Miliyan Dari a kowane wata, don haka ya bukaci a yi masa bayani.
Shugaban Ma’aikatan Ofishin Mataimakin Gwamna ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar na cikin halin kaka-nika-yi Sakamakon masu zagon kasa da suka sanya son zuciya a gaban kishi fiye da sanya bukatar talakawa a gaba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...