Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake ɗage ranar babban taronta na kasa bayan tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairu tun da farko.
Wannan na ƙunshe a cikin wata takarda da jam’iyyar ta aika wa hukumar INEC ɗauke da sa hannun shugabanta na riƙo gwamnan Yobe Mai Mala Buni.
“Muna sanar da hukumar zaɓe cewa jam’iyyarmu ta yanke shawarar gudanar da zaben shiyoyi a ranar 26 ga watan Maris.”
Hakan na nufin an ɗage taron tsawon wata ɗaya
Ba a san ranar gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa ba.