Uwar jam’iyyar APC ba ta yi mana adalci ba – Shekarau

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Sanatan Kano ta tsakiya Kuma Jagoran G7 Malam Ibrahim Shekarau ya ce matakin da uwar jam’iyyar APC ta kasa ta dauka na bada shaidar tabbatar da Abdullahi Abbas a Matsayin Shugaban jam’iyyar APC na Kano da ta yi a Jiya alhamis bai dace ba.
Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wani Sakon Muryar Shekarau da Kadaura24 ta Samu a Sahihin shafinsa na facebook.
Sanata Shekarau yace abun da Uwar jam’iyyar ta yi ya nuna akwai Waɗanda aka dauka yan mowa da yan bora a cikin jam’iyyar, Saboda yadda aka Mika shaidar cin Zabe ga tsagin Ganduje Kasa da awa biyu da Hukuncin kotun daukaka kara.
” Wannnan Matakin babu adalci a Cikin sa duk da mu mun fi Wata biyu da hukuncin kotu a hannunmu ,amma duk da haka uwar jam’iyyar bata baiwa Shugabannin tsagin mu shaidar tabbatar da Shugabancin jam’iyyar ba ” inji Shekarau
Sanata Shekarau ya bukaci uwar jam’iyyar data yi kokarin yiwa Kowa adalci Saboda a Sami dai-daito kamar yadda dake ikirari akoda yaushe.
Sanata Mallam Ibrahim Shekarau, a madadin sauran magoya baya da masoya  ya bayyana cewa sun umarci lauyoyinsu da su daukaka kara bisa hukuncin da kotu ta yi a  jiya Alhamis 17 ga watan Fabrairu 2022.
Haka kuma Sanata Mallam Ibrahim Shekarau ya zargi jam’iyyar APC da rashin adalci da nuna bambanci a tsakanin ‘ya’yanta.
A daya bangaren kuma, Sanata Shekarau ya yi tir da kalamai na rashin arziki da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi ga yan albarka bakwai bayan wannan hukuncin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...