Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta ayyana shiga yajin aiki na sati huɗu a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayyar ƙasar.
Shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Victor Osodeke ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Litinin bayan wata ganawa da majalisar zartarwar ƙungiyar ta yi ta tsawon kwana biyu.
Shugaban ƙungiyar reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, Kano ya ce shugabannin ƙungiyar na jihohoi na kan hanyarsu ta komawa don sanar da ƙungiyoyin nasu halin da ake ciki.