Daga Mukhtar Dahiru
Sanannen matashin dan gwagwarmayar nan wanda yayi suna wajen tofa albarkacin bakin sa kan al’amurran yau da kullum dake faruwa a Najeriya, Comr. Dahiru Mukhtar, ya ce a halin yanzu duk wani dan Najeriya yana cin arzikin gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne na jihar Sokoto.
Comr. Dahiru, ya bayyana hakan ne yau Lahadi a Sahihin shafin sa na facebook, inda yace “Duk wanda ya kwana ya tashi a Najeriya daga shekarar 2014 zuwa yau yana cin arzikin jarumtar gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Mukhtar Dahiru yace Tambuwal shi ne ya jagoranci ceto dimokuradiyyar Najeriya a lokacin da Jonathan ya danne ta zai yi mata yankan Kunkurun Bala”
“Da yanzu ‘yan Najeriya mun zama bayi babu mai iya hawa Intanet ya bayyana ra’ayin sa”
“Wannan kawai ya ci mu sakawa (Matawallen Daular Usmaniyya) da kujerar shugabancin Najeriya 2023” Inji Comr. Dahiru Mukhtar
A makonni biyu da suka gabata ne dai gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa.