Daga Rabi’u Muhd
Babban Magatakardar Kotunan Shari’ar Musulunci ta jihar kano Abdullahi Ado Bayero ya bukaci d ualiban ilimin Sanin fannin shari’ah da su kasance masu Kula da Karatun da suke yi don gudanar da harkokin shari’ah kamar yanda Addinin Musulunci ya tanada.
Abdullahi Bayero ya bayyana hakan ne a wajen taron gudanar da Shari’a a aikace Wanda daliban Kwalejin harkokin Shari’a ta Jihar Kano wato legal.
Babban Magatakardar wanda Alkalin kotun Majistare dake gidan Murtala Tijjani Saleh Minjibir ya Wakilta yace akwai aikin Mai yawa akan daliban Musamman na dage su yi karatu yadda ya dace domin raje kansu Kalubale Idan sun Fara Aikin a fannin Shari’a.
A nasa bangaren Shugaban kwalejin ilimin shari’ah legal na jihar kano Farfesa Balarabe Jakada, Wanda ya Samu wakilin mataimakinsa Auwalu Muhammad Karaye, ya jaddada kudirin su na ganin an cigaba da samar da Daliban shari’ah a fadin jihar nan, Inda yace duk shekara suna yaye dalibai da dama.
Alkalin Babbar kotun Shari’ar Musulunci dake Rijiyar lemo Abdu Abdullahi Wayya ne ya jagoranci gudanar da Shari’ah a aikace a Wannan makaranta.
A karshe wata lauya mai Zaman kanta Barr. Baraka Aliyu Sulaiman Esq tayi jan hankali ga Dalibai dasu zage Damtse wajen samun damar koyon ilimin shari’ah domin samar da Ingancin Shugabanci a jihar nan dama kasa baki daya.