Dansarauniya ya Kasa cika Sharruddan beli, ya na rokon kotu ta sassata Masa

Date:

Daga Zubaida Abubakar Ahmad

 

Mua’zu magaji Dansarauniya wanda yayi kaurin Suna wajen sukar Gwamna Ganduje a Kafafen Sada zumunta har yanzu bai cika sharuddan belin ba, ya kuma shigar da Wani roko a gaban kotu yana rokon kotun ta yi masa sassauci kan sharuddan belin da aka Sanya masa.

A cewar wata majiya mai tushe daga ma’aikatar shari’a ta Kano wadda Jaridar , Justice Watch News ta tattaro, ta ce Lauyan Dansarauniya, Barista Garzali Datti Ahmad ya shigar da rokon ne a ranar 9 ga watan Fabrairun 2022 Mai dauke da sa hannun Lauyansa Garzali Datti Ahmad, inda ya yi rokon kotu ta sake duba sharuddan belin da ta Sanyawa Dansarauniya tun farko .

Hakan na iya dakatar da rahotanni masu karo da juna da ke yawo a wasu gidajen rediyo da kafafen sada zumunta dangane da batun belin Dansarauniya.

Idan dai za a iya tunawa, Alkalin Kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari ya Amince da bayar da belin Mu’azu Magaji bisa sharuddan ajiye kudi Naira miliyan 1 da gabatar da mutane 2 Waɗanda zasu tsaya masa, wadanda suka dagacin Dansarauniya baya ga kwamandan Hisbah ko kuma babban limamin karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kotun ta kuma umurci Mua’zu magaji ya ajiye fasfo dinsa na kasa da kasa a wurin rajistaran kotun.

Rahotannin sun tabbatar da wanda ake tuhumar har yanzu bai iya cika sharuddan ba, domin kwamandan Hisbah ko kuma babban limamin Dawakin Tofa ba Wanda ya halarci wajen sanya hannu kan takardar belin Dansarauniya ba.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa wanda ake kara an gurfanar da shi ne a gaban kuliya bisa laifin bata Suna, cin mutunci, karya da kuma tada hankali.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin da ake Zarginsa.

Lauyan masu kara, Barista Wada A Wada, babban Lauya a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022 a shafinsa na Facebook.

Wada ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya saka hoton Ganduje tare da wata mace da har yanzu ba a tantance ba a shafinsa na Facebook.

A cewar sa, laifin ya ci karo da sashe na 392, 399 da 114 na kundin laifuffuka.

An dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga Maris, 2022 don ci gaba da Shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...