Fashewar tukunyar Gas din girki tayi sanadiyyar mutuwa mutum 1 da jikkata wani a kano

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakariyya
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon fashewar iskar gas da ta afku a kauyen Ijarawa da ke karamar hukumar Bichi a jihar kano.
 Kadaura24 ta rawaito Wani mutum daya ya tsira daga hatsarin.
 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a Kano.
 Ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar 8 ga watan Fabrairu.
 “Mun samu kiran gaggawa daga Sufeto Daiyabu Tukur da karfe 07:46 na safe cewa wata mota da ke dauke da silindar gas din dafa abinci ta fadi a kan hanya kuma daya daga cikin bututun ya fashe.
 “Bayan samun labarin, mun aika tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru Cikin gaggawa da misalin karfe 8:00 na safe domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.
 Ya ce motar J5 ta kasuwanci mai lamba FB 52 LAD ta nufi Katsina daga Kano kuma tana jigilar iskar gas din girki ne.
 Abdullahi ya ce hatsarin ya rutsa da mutane biyu, Maikano Muhammad mai shekaru 45, wadanda suka mutu yayin da Abdullahi Usman mai shekaru 40, an ceto shi da ransa.
 “Dukkan wadanda abin ya shafa an mika su ga Usman Usman na ofishin ‘yan sanda dake Bichi.
 “Ana binciken musabbabin lamarin,” in ji shi.
 Solacebase ta rawaito Jami’in hulda da jama’a ya yi kira ga direbobin da suke daukar isar gas din da su kara taka-tsantsan da yin tuki cikin kulawa domin gujewa afkuwar hadurran tituna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...