Kisan Hanifa: Gwamnatin Kano za ta baiwa waɗanda ake zargi lauya

Date:

 

Babban wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, ya faɗa wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta sama masa lauyan.

“Ba mu da lauya a yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina roƙon gwamnati ta ba mu lauya,” in ji Abdulmalik a zaman kotun na yau Litinin.

Su ma sauran mutum biyun; Fatima da Hashin Isiyaku, sun amince da abin da Abdulmalik ya faɗa na neman lauyan.

Lauyan gwamnati Musa Lawal ya ce gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka buƙata. Da ma dai haka doka ta tanada saboda laifin da ake zargin su da aikatawa mai girma ne.

BBC Hausa ta rawaito Mai Shari’a Sulaiman Na Abba ya ɗaga zaman shari’ar zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da ƙarfe 2:00 na rana.

A watan da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama mutum uku da ake zargi da sacewa da kuma kashe ‘yar shekara biyar ɗin a unguwar Dakata Kawaji da ke birnin Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...