APC ta samar da tsarin raba mukaman jam’iyyar tsakanin Ganduje da Shekarau

Date:

Daga Zakariyya Adam Jigirya
 Jam’iyyar APC ta samar da wani tsari na raba mukaman jam’iyyar tsakanin bangarorin da gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Ganduje ke jagoranta da kuma na sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau.
 Bangarorin biyu dai sun yi ta gwabzawa kan yadda jam’iyyar zata kasance wajen Shugabantar jam’iyyar a Kano.
Bayan tashi daga taron gaggawar da kwamitin riko na jam’iyyar APC ta Kasa ya kirawo karkashin jagorancin Mai Mala Buni, wanda aka gudanar a daren ranar Asabar, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti zuwa Kano domin tabbatar da an bi sabon tsarin rabon mukaman jam’iyyar a Kano.
 A wata sanarwa bayan taron da aka yi a daren ranar Asabar, mai magana da yawun Malam Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samar da tsarin Sanya kowa Cikin harkokin jam’iyyar ta APC a Kano.
 Ya ce za a sanar da duk bangarorin biyu halin da ake Ciki a ranar litinin.
 “Za a kafa kwamiti mai karfi daga sakatariyar jam’iyyar kuma a tura shi Kano don tabbatar da bin ka’ida da aiwatar da tsarin da za a yi a ranar Litinin,” in ji Sule.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...