Daga Adamu Bichi
Majalisar dokokin jihar Zamfara na shirin tsige mataimakin Gwamnan jihar Barista Mahdi Ali Gusau.
Wannan dai ya biyo bayan zarginsa da wasu laifuka guda takwas da kundin tsarin mulkin ƙasa ya amince a tsige mai irin wannan laifukan.
Shugaban majalisar dokokin jihar Nasiru Ma’azu Magarya ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Daily News24 ta Nambobin majalissa sun gabatar da kudurin cewa a tsige shi bisa wasu dalilai, saboda haka za mu zauna mu yi nazari kafin mu aiwatar da hukunci na gaba” a cewar Magarya.
Ana zargin hakan na da nasaba da ƙin komawar mataimakin gwamnan zuwa jam’iyyar APC bayan da Gwamna Bello Matawalle ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.