Kwamitin su El-Rufa’i ya baiwa Buhari shawarar kara farashin man fetir zuwa 302

Date:

Watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021, kamar yadda jaridar TheCable ta labarto.

Jaridar ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.

A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.

BBC Hausa ta rawaito Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...