An gudanar da taron tunawa da yan mazan jiya a kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar kano ta bukaci jami’an tsaron dake kasar nan da su yi amfani da ranar ta tunawa da yan mazan jiya ta shekara 2022, wajen auna irin aiyukan da suke gudanarwa domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da ya halaccin taron tunawa da tsafaffin sojojin Nigeria wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na daya dana biyu dama yakin basasa.

Gwamnan yace idan akai la’akari da gudunmawar da tsafofaffin sojojin suka bayar akwai bukatar jami’an tsaron wannna lokaci su yi koyi da su wajen sadaukar da kai domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nigeria.

Yace ya zama wajibi a rika yiwa tsofaffin sojojin addu’o’i saboda da rawar da suka taka wajen tabbatuwar Nigeria matsayin kasa daya dunkulalliya.

Ganduje ya kuma bada tabbacin gwamnatin jihar kano zata cigaba da tallafawa Kungiyar tsofaffin sojojin da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin kare martabar kasar nan .

Kadaura24 ta rawaito yayin taron dai an gudanar da addu’oi da fareti tare kuma da sanyan fure Wanda ke nuna tausayawa da kuma yabawa tsofaffin sojojin, taron dai ana gudanar da shi duk ranar 15 ga watan janairun ko wacce shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...