Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Wasu ma’abota bibiyar manhajar kallo ng ta wayoyin hannu a Android da ta na’urar Computer ta laptop sun bayyana gamsuwarsu bisa yadda manhajar Kallo.ng ke debe musu kewa, da kuma sanya nishadi, ilmantarwa da kuma nishadantarwa.
Malama Aisha Mahmoud mazaunuyar garin kano ta shaidawa jaridar time express Nigeria cewar tun daga lokacin da sauke manhajar Kallo.ng a wayar ta Android take cikin nishadi, domin kuwa duk lokacin da take son Kallon fina-finan Hausa gasu nan sai wanda ta zaba ” gaskiya manhajar Kallo ng tayi”
Mukhtar Khalil maaikacin gwamnati ne, amma yace yana amfani da manhajar wajen kallon fina-finan kannywood lokacin da yake hutawa a gida, yace babu shakka wadanda suka kirkiri wannan Manhaja sunyi rawar gani kuma dole a jinjina Musu.
Ko ta yaya ake sauke manhajar kalloTV?
Idan aka shiga shafin Play store a wayar Android sai a je “search” sai a rubuta kallo.ng za’a ga tambarin Kallo.ng ya fito, sai a danna download, wato ana so a sauke manhajar ke nan a waya, to daga nan idan an sauke shi ke nan kallo a saukake, da Data kadan sai ayi kallo Mai yawa.
A zantawar da jaridar time express Nigeria ta yi da shugaban kamfanin Space crafts media wadanda su ne suka kirkiri Manhajar Hajiya Maijidda Shehu Modibbo tace sun kirkiri manhajjar ce don saukakawa ma’bota kallon fina-finan hausa su zaba su dare, su kuma kalli duk fim din da suke so a ko ina suke a fadin duniya ta wayar hannu wacce ake kira Android.