Wata kungiya a Kaduna ta Roki Buhari ya tsige Shugaban hukumar Daraktoci na Cibiyar Kula da Kunne ta Gwamnatin Tarayya

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Wata Kungiya Mai rajin ganin kawo dai-daito a Jihar Kaduna ta roki Shugaban kasa Muhd ​​Buhari da ya cire Shugaban Hukumar Daraktocina Cibiyar kula da kunne ta Gwamnatin tarayya dake jihar kaduna Alhaji Garba Sani Dankani bisa zarayin son rai da yake sakawa a harkokin Cibiyar.
 Da yake ganawa da Manema labarai a madadin ‘ya’yan Kungiyar Kwamaret Richard Ostin yace tun daga lokacin da aka nada Dankani akan mukamin cibiyar take ta Samun komawa bayan Saboda yadda yake nuna rashin kwarewa a jagorancinsa.
 Richard yace Suna so a cire Alhaji Garba Dankani ne Saboda da tarin Matsaloli da Mayar da hannun Agogo baya da yake yi wajen ciyar da Cibiyar gaba don tayi gogayya da takwarorinta na duniya.
 Yace ya hanna Daraktocin Cibiyar su Gudanar da aikin su yadda ya kamata, Kuma yana tafiyar da Cibiyar tamkar tasa baya bin duk Wasu ka’idoji da dokokin cibiyar, Kawai yana al’amuran sa gaba gadi ba bisa doka ba.
 “Ko a kwanakin baya sai da yayi Yunkurin dakatar da Shugaban Asibitin Dr. Mustapha, kawai Saboda son rai Wanda Ma’aikatar Lafiya ta Kasa ta taka Masa burki Sabon rashin bin ka’ida wajen yin wannna danyen aikin”. Inji Richard
Kungiyar tayi zangin cewa tun lokacin da Dankani ya zama shugaban hukumar daraktoci a asibitin bai kawo wani tsari ko guda daya ba Wanda zai ciyar da cibiyar gaba, sai ma koma baya da ciyar take samu .
Duk duniya hukumar daraktoci babu ruwanta da abun da ya shafi gudanarwar ma’aikata ,amma shi sun zarge shi da shiga cikin harkokin gudanarwa cibiyar dama Ma’aikatan cibiyar, Wanda suka ce hakan ba daidai bane kuma ba za su lamunci hakan ba.
” Irin abubuwan da Alhaji Dankani yake yi a Asibitin zai iya kawo hatsaniya a cikin asibitin Wanda kuma hakan zai iya shafar jihar Kaduna baki daya ,Wanda kuma hakan mayar da hannun agogo baya ne ga kokarin da gwamna Malam Nasiru Ahmad El-rufa’i yake na tabbatar da zaman lafiya a jihar Kaduna” inji Richard
Daga karshe Kungiyar ta ce duba da irin wadancan dalilai da suka bayyana, su ke bukatar Ministan lafiya da Shugaban kasa Muhd Buhari ya bada izinin a gudanar da bincike don gano gaskiyar abun da suka zargin Shugaban hukumar daraktocin ciyar kula da kunne domin daukar matakin dakatar da shi koma cire shi daga mukamin nasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...