Tallafawa Al’umma Yasa Kungiyar Mu Hadu Mu Gyara ta Jihar Kano ta Karrama Falakin Shinkafi Amb.Yunusa Yusuf

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar Mu Hadu Mu Gyara ta Jihar da Hadin gwiwar Kungiyar Muryar al’ummar Yakasai sun Karrama Falakin Shinkafi Amb. Yunusa Yusuf Hamza bisa kokarin da yake wajen tallafawa Rayuwar al’ummar Yakasai da ma Jihar Kano baki domin inganta Rayuwar su.

 

Sarkin Dawaki Mai tuta Alhaji Bello Abubakar ne ya Mika Masa Lambar yabon Yayin taron bude ofisoshin Kwamitin Yakasai da na Kwamitin Cigaba unguwar Yakasai .

 

Da yake Jawabi Sarkin Dawaki Mai tuta yace dama kamata yayi a rika karawa Waɗanda suke taimakawa al’umma kwarin gwiwa domin su cigaba da Aikin da suke na tallafawa Al’umma.

 

Ku kula da Malaman da Zaku Kai ‘ya’yanku wajensu – Falakin Shinkafi ya fadawa Iyaye

Yace a Wannan Lokaci akwai buƙatar mawadata su rika tallafawa mabukata Saboda ana cikin Mawuyacin Halin, a don Haka ne yayi Kira ga Sauran mawadata a unguwar Yakasai da Jihar Kano baki daya da su yi koyi da irin aiyukan jin Kai da Ambassador Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafi) yake gudanarwa.

Shi ma a Jawabinsa Shugaban Kungiyar Mu Hadu Mu Gyara Malam Mahmoud Ali yace sun zabo Amb. Yunusa Yusuf ne bisa yadda yake sadaukar da abun da Allah ya bashi wajen taimakawa Masu karamin karfi dake cikin al’umma.

“Falakin Shinkafi Mutum ne karimi da baya gudun Matsalolin mutane Kuma , baya wulakanta Kowa shi da tausayin na Kasa , Wannan ce tasa muka Karrama shi a Wannan rana domin Kara Masa kwarin gwiwa da Kuma nunawa yabawa da aikin da yake don mawadata su yi koyi.” Inji Mahmoud Ali

Yace zasu cigaba da zabo al’umma daban-daban Waɗanda suke taimakawa Mutane domin Karrama su, domin na baya su yi koyi da aiyukan tallafawa Al’umma.

Da yake nasa Jawabin Ambassador Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafi) ya godewa Allah (S W A) da Kuma Shugabannin Kungiyoyin bisa Karramawar da sukai Masa a Wannan Lokaci.

Ambassador Yunusa yayi fatan Kungiyoyin zasu cigaba da aikin hidimtawa al’umma, Inda yace babu abin da yakai taimakawa al’umma a don haka ne yace Wannan Karramawar zata kara masa kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa al’ummar Yankin dana Jihar Kano baki daya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...