Shirya taron zumunci zai wanzar da zaman lafiya a ƙasa – Ɗan kadan Kano

Date:

Daga. Nasiba Rabi’u Yusuf
Ɗan kadan Kano kuma Dan majen Gwandu Alhaji Bashir Ibrahim  Muhammad ya buƙaci al’umma da su riƙi zumunci a matsayin abinda zai ƙara kyautata alaƙarsu da yan uwan su a duk inda suke.
KADAURA24 ta rawaito Alhaji Bashir Ibrahim ya bayyana hakan a ranar Litinin, a wajen taron zuriyar Marigayi Moddibo Mahmud da kuma gabatar da littafin tarihin zuri’ar.
Ɗan kadan Kanon ya ce, kowacce zuri’a tana yin ƙarko ne a duk sanda ƴaƴan cikinta suka ɗauki matakan ingantata musamman ta hanyar shirya taruka.
“Muna sane da tarihin yadda kowacce zuriya ke fara da kaɗan, sai kuma ta bazu zuwa sassan duniya ta ci gaba da yaɗuwa ta hanyar hayayyafa”.
Zuri’ar Moddibo ta zo Kano ne tun daga zamanin marigayi sarki Abdullahi Maje Karofi ga shi a yanzu zuriyar ta fara tattaro kanta ta hanyar bincike da tuntuɓa”.
Alhaji Bashir Ibrahim ya kuma ce, ta hanyar shirya taron dangi ne za a san yawan zuri’a kuma zumunci zai ƙara danko da kuma samu haɗin kani da zaman lafiya.
Taron ya samu halartar ɗaukacin ƴaƴa da jikoki daga sassa daban daban na ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Daura ya nuna inda za’a binne shi idan ya rasu.

  Mai Martaba Sarkin Daura dake jihar katsina Alhaji Dr....

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...