Daga Abdulrasheed B Imam
Gwamnatin Jihar Kano ta rabawa Mabukata dari hudu buhunhunan shinkafa domin ragewa al’umma Musamman masu karamin karfi halin matsin rayuwa da ake Ciki.
KADAURA24 ta rawaito Darakta Janar na Hukumar Zakka da Hubsi ta Jihar Kano Alhaji Safyan Ibrahim Gwagwarwa ne ya bayyana hakan yayin Kaddamar da rabon Kayan Wanda aka gudanar a harabar Hukumar Shari’a ta Jihar Kano.
Alhaji Safyan Gwagwarwa yace an rabawa Mutanen shinkafar ne duba da halin Matsayin rayuwa da ake fama da shi a wannna Lokaci, inda yace rabon Kayan Zai sauƙaƙawa al’ummar da suka Amfana da tallafin.
Yace Hukumar ta dade tana gudanar da irin Wannan aiki, Wanda dama yana daga Cikin aiyukan ta taimakawa Masu karamin karfi domin rage musu radadin talauci.
Babban Daraktan yace Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya Samar da kudin da aka sayo Kayan da aka raba, Inda ya yabawa Gwamnan Saboda irin tallafin da yake baiwa Hukumar akan Kari ba tare da gajiyawa ba.
A Jawabinsa Shugaban Hukumar Zakka da Hubsin Sheikh Usman Yusuf Makwarari yace ya zama wajibi su yabawa Gwamnan Ganduje Saboda irin kulawa da goyon bayan da yake baiwa Hukumar domin ta taimakawa Mabukata a Jihar nan.
Shi ma da yake Kaddamar da Shirin Shugaban Hukumar Daraktoci na Hukumar Shari’a ta Jihar Kano Sheikh Sayyadi Bashir Usman Zangon Bare-bari ya bukaci mawadata da suke Cikin al’umma da su rika tallafawa Mabukata ,Inda yake yin hakan zai iya Zama sanadiyyar yayewar matsin Rayuwa da Matsalar tsaro da ake fuskanta a Kasar nan.
Sheikh Zangon Bare-bari ya Kuma hori al’ummar Jihar Kano dana kasa baki daya su dage da yin addu’o’in Samun Zaman Lafiya da Samun saukin halin Matsayin rayuwa da ake ciki a Wannan Lokaci.
Kimanin Magidanta 400 ne Suka Amfana da tallafin buhunhunan shinkafa daga Kananan Hukumomi 44 dake fadin Jihar Kano.