Kasurgumin dan bindigar da ya addabi jama’ar yankin arewa maso yammacin kasar nan Bello Turji, ya nemi yin sulhu da gwamnati, sakamakon barin wutar da dakarun. sojojin kasar ke cigaba da yi musu a dazukan da suke boye.
Wata majiya ta ce Turji ya nemi yin sulhu gami da alkawarin ajiye makamansa ne, cikin wata wasika da ya aike da nufin isar da it aga gwamnan Zamfara Bello Matawalle da kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Cikin labarin da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Jaridar Daily Trust da ke Najeriya ta ce wani mazaunin yankin Shinkafi a jihar Zamfara ya tabbatar mata da gaskiyar labarin.
Tun daga ranar Alhamis 16 ga watan Disamba, dakarun Najeriya ke yi wa ‘yan bindiga luguden wuta a kauyen Katanga da ke jihar Sokoto a karamar hukumar Isa.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce babban kwamandan sojin dake kula da runduna ta 8 Manjo Janar Uwem Bassey ne ke jagorantar tawagar sojoji tare da manyan jami’an sa a cikin motocin yaki sama da 20, wadanda suka yi wa ‘yan bindigar kofar rago, yayin da sojin sama ke taimaka musu da ruwan wuta ta sama.
Jihar Sokoto na daya daga cikin Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ‘yan bindiga suka mamaye wasu sassanta, inda suke kai munanan hare hare suna kashe mutane.
Makwanni biyu da suka gabata, ‘yan bindigar suka kai kazamin hari karamar hukumar Sabon Birni inda suka kona wasu matafiya sama da 40 a cikin motar su.