Bayan kotu ta ba da belin sa, Mustapha Jarfa ya ce ba zai sake cin zarafin wani ba

Date:

Daga Ibrahim Rimin kebe
Kotun Majistry  mai Lamba ta 58 dake unguwar Nomandsland
Karkashin jagorancin mai sharia Alh Aminu Gabari ta bada belin dan Siyasar nan Mai suna Mustapha Bature Wanda aka fi sani da Mustapha jarfa
KADAURA24 ta rawaito tun a Zaman kotun da ya gabata aka sanya wannan rana ta 13/12/2021 domin nazari akan belin mustapha jarfan kuma a zaman kotun na wannan rana mai sharia Aminu Gabari ya amince da bada belin wanda ake zargin.
Bayan da ya saurari bangarorin biyu ne sai mai Shari’a majistiri Aminu Gabari ya damkashi a hannun beli amma fa bisa sharadin zai kawo ‘yan’uwansa na jini guda biyu.
Indai ba’a manta ba Mustapha Jarfa anganshi  cikin kunshin wani vedio inda yake kalaman batancin ga shugaban jam’iyyar APCn jihar kano Hon Abdullahi Abbas.
Wanda daga bisani ya fito cikin wani sakon murya a makwannin baya, bayan fitowa daga kotu yayin wani zama da tayi.
Bayan fitowa daga kotun munyi kokarin jin ta bakin bangarorin biyu sai dai hakan bai samu ba.
Daga Karshe dai an damka jarfan a hannun jami’in gidan gyaran hali
Aic Abbas Abubakar kafin ya cika waccan sharadi na kotun.
Bayan bada belin, Mustapha jarfa ya ce ba Zai sake aika ta Laifin cin zarafin Wani ba , ya kuma godewa Waɗanda Suka bada Gudunmawa wajen karbar belinsa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...