Wata kungiya ta rarrabawa masallatai 42 kayan kula da Masallaci a kano

Date:

 

Daga Abdurrashid B Imam

Wata Kungiya mai suna alkalami ya zarce takobi da gwaiwar gaskiya dokin karfe dake unguwar marmara karkashin jagorancin malam Naziru Musa Shehu Marmara sun rarraba butoci, tabarmi, tsintsiyoyi harma da kwanikan abincin da kofunan da za a rika amfani dasu in anyi rasuwa ga masallatan dake kananan hukumomin munincipal dala gwale.

KADAURA24 ta rawaito Malam Naziru ya bayyana cewa sun raba kayan ne don yi koyi ga magabatan su Waɗanda suke tanadarwa al’umma abubun da suke bukata a masallatai ko kuma Waɗanda za a iya amfani da su idan an yi rashin wani Mutum.

Shugaban kungiyoyin ya Kara da cewa sun yi amfani da kudaden da suka samu a ranar asabar din data gabata a yayin kaddamar da littafin so ko kauna za a yiwa Annabi domin yiwa addinin Musulunci hidima .

Malam Naziru Marmara yace dama sun dade suna amfani da damar da suke da ita wajen taimakawa don tsaftacewa da inganta masallatai a Jihar Kano.

Ya Kuma yi kira ga kungiyoyin da ake kafawa na bogi dasu ji tsoron Allah su tina akwai ranar da Allah zai tambayi Waɗanda suka kafa su, tare da buƙatar al’ummar Unguwanin da aka kai kayan dasu baiwa Kayan kulawar data dace domin su dade su na amfanarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...