Al’ummar Garin Guringawa sun Zargi Shugaban K/H Kumbotso da yanka filaye a tsohon Asibitin Garin

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
Al’ummar garin gurungawa dake yankin karamar hukumar kumbotso sun zargi shugaban karamar Hassan Garban Kauye Farawa da auna tsohon asibitin garin domin yanka filaye a cikinsa.
Gamayyar kungiyoyi 13 ne da garin suka nuna rashin maincewarsu ga wannan mataki da shugabancin karamar hukumar ta kumbotso yake Shirin dauka, Wanda al’ummar garin suka ce hakan zai kai musu tasgaro musamman ta fuskar tsaron al’umma.
Hon. Dahiru faruq guringawa yana daga Cikin Waɗanda wakiliyar Kadaura24 ta zanta da su yace sun dade Suna Amfani da tsohon Asibitin ta fuskar mayar da shi helkwatar Jami’an Vigilantee don Inganta tsaron al’ummar yanki.
“Mun yi mamaki da muka fa an Zo ana auna Asibitin saboda mun San irin kokarin da gwamna Ganduje da Shugaban Karamar Hukuma Hassan Garban Kauye wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.” Inji Dahiru Faruq
Yace kafin su Fara Amfani da tsohon Asibitin sai da suka Sanar da Uban Kasa dagacin Garin na guringawa tare Kuma da kashe kudi sama da Naira dubu 150 don dai su  gyara Kuma yan sintirin yankin su Sami inganta harkokin tsaro a yankin.
“Muna da tabbacin Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Bai San da Wannan Lamari ba, hakan tasa muke zargin ko wasu ne suke so su bata masa Suna, don haka muke Kira ga Garban Kauyen yasa a binciki lamarin.
Kadaura24 ta tuntubi shugaban karamar hukumar kumbotson Hassan Garban Kauye Farawa ta hannun Mataimakinsa ta fuskar yada labarai Shazali Sale Farawa don Jin ko yasan da Wannan matsalar,in Kuma sun Sani to Ina dalilin yin Haka ? .
Garban Kauyen yace bashi da masaniya akan batun ,amma zai binchika domin Sanin hakikanin Faruwar  Al’amari.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...