An bude gasar wasan kwallon kafa ta kafafen yada labarai dake Kano

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa
A ranar Juma’a nan ne da misalin 4:27 na yamma ne aka fara gudanar da wasan gasar kwallon kafa ta kafafen yada labarai 13 dake jihar kano, a idan aka take wasan a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon Gari a jihar Kano tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Gidan Radiyo Nigeria Pyramid FM dake Kano da kungiyar kwallon kafa ta gidan Abubakar Rimi Talabijin dake Kano.
Da misalin karfe 5:26 Kungiyar Kwallon kafa ta ARTV ta ci Gidan Radio Nigeria Pyramid Fm 1 – 0 .
Dama dai Kusan duk Shekara Kungiyar marubuta labarin wasanni ta Jihar Kano tana Shirya irin wannnan Wasan domin Kara dankon Zumunci a tsakanin Kafafen yada labarai dake jihar Nan.
Waɗanda Suka halacci Bude gasar Wasun hadar da Mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya Wanda Shugaban Hukumar kawata birnin Kano Hon Abdullahi Tahir El-kinana ya wakilta sai Shugaban gidan Radiyo Pyramid FM Kano Abba Bashir da takwararsa Shugabar gidan Abubakar Rimi Talabijin dake Kano Hajiya Sa’a Ibrahim da Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano Ibrahim Galadima .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...