Daga Rukayya Abdullahi Maida
Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro, guda cikin malaman da su ka yi mukabala da malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya rasu a .
Rahotanni da Kadaura24 ta samu sun nuna cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren jiya Laraba, sakamakon haɗarin mota da yayi a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Lokacin da akai mukabala da Abduljabbar Kabara Malam Mas’ud Hotoro shi ne ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya a zaman .
za dai a yi jana’aizar malam Mas’ud din ne yau Alhamis da misalin karfe 02:00 na Rana a gidansa da ke Hotoro.