Inganta Aiki: Dangote ya shiryawa Yan Jaridu 60 Bitar kwanaki Uku

Date:

Daga Yakubu Abdullah

 

Kamfanin Dangote ya fara wani shiri na horas da ‘yan jaridu 60 a Kano, a wani bangare na sauke nauyin al’ummarbda yake tare da su.

A cewar kamfanin, an Shirya taron bitar ne da nufin kara Ilimi ga Manema labarai kan sabbin hanyoyin fasahar Zamani  don inganta harkokin yada labarai ga yan jaridun da suka fito daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Sokoto, Katsina, Kebbi, Kano, Kaduna, da kuma Jigawa

Bitar haɗin gwiwa ce da cibiyar horaswa akan ayyukan yada labarai ta Folio Media and Creative Academy kuma an gudanar da bitar a baya a wasu shiyyoyin ƙasar nan.

Taron na kwanaki uku an yi masa taken da “Haɗewar aikin jarida”

A taron da aka fara gudanar da horon a Kano ranar Laraba, shugaban rukunin kamfanin, Branding and Communication, Anthony Chiejina, ya ce an shirya bitar ne domin inganta kwazon ‘yan jarida kan dabarun yada labarai na Zamani.

Ya ce horon zai taimaka wajen samar wa manema labarai damar tunkarar kalubalen da ke tattare da tsoho salo yada labarai zuwa sabbin dabarun yada labarai n Zamani.

Ya bayyana cewa akwai alaka mai kyau tsakanin kamfanin da kafafen yada Labarai dake Kasar nan.

Mai kula da wannan shiri a Folio Media and Creative Academy, Alabi Pius, ya ce cibiyar (FMCA) ita ce ta horar da Folio Communications Plc.

Mawallafin na jaridar Daily Times, ya kara da cewa an shirya wannan horon ne domin baiwa ‘yan jarida da shugabannin kafafen yada labarai da jami’an hulda da jama’a damar Sanin sabbin dabarun yada labarai na Zamani.

A  jawabinsa, wani malami a Jami’ar Bayero Kano, Mai Suna Dr. Mukhtari Magaji, ya bukaci ‘yan jarida da su yi shirin sauyawa zuwa Sabon tsarin yada labarai na zamani, domin fasahar za ta kara musu karfin gwiwa da kuma sanya su cikin sabuwar duniya.

Dokta Magaji ya bayyana cewa hada aikin yada labarai na nufin amfani da rubutu, sauti, da bidiyo ta hanyar kafar sadarwa guda ɗaya.

Sauran malaman da za su yi jawabi a shirin horaswar sun hada da Dr. Bala Muhammad, tsohon dan jarida a kafar yada labarai ta BBC da ke Landan kuma malami a Jami’ar Bayero Kano; da kuma Dr. Saminu Umar, shima malami a wannan jami’ar.

A nasa jawabin, wani da ya halarci taron kuma wanda ya samar da shafin Jaridar “Good Governanc”, Dakta Aliyu Machika, ya ce horon ya yi dai-dai da lokacin da ake bukatarsa domin zai baiwa manema labarai a shiyyar Arewa maso Yamma damar kara kaimi da kuma kara musu karfin tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

A wani mataki na tabbatar da bin ka'idoji tare...

Da dumi-dumi: NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

  Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu...

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...