Daga Nasir Ahmad
Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa ta mika sakon Ta’aziyya da Jajantawa ga Iyalai da “Yan uwan mutanen guda 43 da suka sami Hatsarin Jirgin ruwa a Dam din Bagwai.
Sanarwar mai dauke dasa hannun Sakataren yada labarai na Kungiyar ta Kasa Abubakar Balarabe Kofar Naisa wadda Kuma ya aikowa Kadaura24 tace Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta samu kanta cikin dimauta da kaduwa a lokacin data samu labarin faruwar al’amarin a yammacin Talata ta karshen watan Nuwamba.
Kungiyar Samarin Tijjaniyya tayi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya gafarta musu ya karbi shahadarsu, sannan kuma wadanda suka samu jirkata Allah ya basu lfy yasa yazama kaffara a garesu.
Game da wadanda ba’a ga Gawarwakinsu ba kuwa kungiyar Samarin Tijjaniyya tayi addu’ar Allah ya bayyana gawarsu domin suma ayi musu janaiza kamar yadda addinin musulunci yayi tanadi.
Kazalika kungiyar taja hankalina masu rike da shugabancin al’umma dake wannan yanki su dauki matakin kare afukuwar wannan al’amri anan gaba kasancewar hakan ya taba faruwa shekaru 13 da suka gabata lokacin da za’a kai wata Amarya gidan mijinta bayan an kammala bikin auren.
Shi dai wannan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Talata data gabata ya faru ne sakamakon ziyarar bikin Mauludi Annabi Muhammadu da dalibai da malaman makarantar Islamiyya dake kauyen Badau za su je zuwa garin Tofa.
Wanda dole ne sai an tsallaka wannan kogi na Bagwai sannan za’a samu damar zuwa wasu kauyukan dake makwabtaka da wannan gari.
A don hakane kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa karkashin jagorancin Shugabanta na kasa ya bukaci Gwamnati ta samar da wata hanya mafi sauki domin ceto rayuwar al’ummar wannan yanki.