Daga Maryam Khamis Lajawa
Tuni Kwamitin sulhun ta yan Jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Adamu sun iso Kano domin Sulhunta Bangaren Gwamnan Kano Ganduje da na Sanata Malam Ibrahim Shekarau.
Uwar jam’iyyar APC ta Kasa dai ta kafa Kwamitin sulhun Yan jam’iyyar ne Saboda irin Rikicin da aka samu a gabanin zaben Shugabannin jam’iyyar APC na jihohi da akai.
Kadaura24 ta rawaito Cewa an Sami ruke-rike a jihohi daban-daban na Kasar nan a jam’iyyar APC,Inda Wasu jihohin aka zaben Shugabannin jam’iyyar Guda bi-biyu Wasu Kuma uku.
A Kano ma dai an sami irin waccan Matsala,Inda tun gabanin zaben Shugabannin jam’iyyar na Jihar Wasu Yan Majalisun tarayya daga Kano karkashin jagorancin Sanata Malam Ibrahim Shekarau Suka Kai korafi ga Uwar jam’iyyar Cewa ba a yi musu adalci a tafiyar da jam’iyyar keyi a Kano.
A Wata ganawa da Shugaban Kwamitin sulhun Sanata Abdullahi Adamu yayi da Manema labarai a Ranar Juma’ar data gabata yace zasu fara Aikin nasu ne da Kano Saboda muhimmancin da Kano ke da shi a Siyasar Kasar nan.
Yanzu haka dai Wakilin Kadaura24 yace ya ga shigowa Kwamitin Jihar Kano,sai dai ba a fadi Inda za’a gudanar Zaman sulhun ba . Amma dai an tanadi kyakykyawan tsarin inganta tsaro Yayin Zaman don gudun kada a Sami Masu tada tarzoma.