Daga Saminu Ibrahim Magashi
Gamayyar wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka hadar da Yes Concept da kuma Asesa sun hada karfi da karfe a yunkurinsu na tallafawa matasa da kuma kananan yara.
Tun da fari dai sun shiryawa yaran dake gidan gyaran hali da tarbiyya na kanann yara horaswa kan sana’oi natsawon watanni uku Wanda Kuma a yau Suka kammala karbar horaswar Kuma Suka biyawa wasu daga cikin yaran tarar kudin da aka yanke musu a kotu.
Da take bayani shugabar kungiyar Mrs Bilkisu Bala tace sun yi duba ne da cewa yaran su ne kashin bayan kowacce al’umma, tace Saboda haka ne suka ga dacewar zabo irin wannan Yara na gidan gyaran hali domin koya musu sana’o’in Saboda idan yaran sun fito ya zamana suna da sana’oin dogaro da Kai.
Bilkisu Bala tace Idan yaran Suna da sana’o’i hakan zai kwantar da hankulansu wajan hana su komawa su aikata lefi.
Taron dai ya samu halartar mutane da dama ciki harda babbar director a ma’aikatar mata da kananan yara da kuma walwalar al’umma ta jihar kano da dai sauran muhimman mutane da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.