Daga Jidda Abubakar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yanke hukunci Dangane da Ranar da jam’iyya mai mulki ta APC ta Kasa zata gudanar da Babban taron jam’iyyar ta kasa.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya shaida wa manema labarai hakanda bayan kammala taron gwamnonin, Inda yace za su nemi ganawa da shugaban kasa domin Sanya ranar da ta dace.
Ana kyautata zaton cewa Gwamnonin za su kuma nemi goyon bayan Shugaban kasa kan yadda ake ta cece-kuce a kan batun Zaben fidda gwani na kato bayan Kato a cikin jam’iyyun siyasar Kasar nan tsakanin ‘yan majalisar dokokin Najeriya da jam’iyyun siyasa ciki har da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Haka kuma Gwamnonin sun bayyana ji dadinsu Kan yadda zaben Gwamnan Anambra ya gudana cikin kwanciyar hankali.