Sanata Barau Jibril ya Sauke kabakin arziki a Kannywood

Date:

Daga Habiba Bukar Hotoro

 

Sanatan Kano ta arewa Sanata Barau Jibril ya bada tallafi ga Yan masana’antar Kanywood domin su bunkasa sana’ar su ta Fina-finan Hausa.

 

 

Dama dai Sanatan ya yiwa Yan masana’antar ta Kannywood alkawarin basu tallafi Wanda ba’a taba Samun Wani Dan Siyasa da ya basu ba .

 

A Jawabinsa yayin taron Wakilin Sanata Barau tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya bada tabbacin Sanatan Zai cigaban da bada irin wannna tallafi ba ga Yan Kannywood Kadai ba har da Sauran Masu gudanar da sana’o’i  a Jihar Kano.

 

Kayan da Sanata Barau Jibril ya rabawa Yan Kannywood sun hadar da :

 

Motoci Guda 17
Babura 100
Komfuta 80
Kamara 5
Generator 5
Kayan Studio 5
Kayan Light 5
Dudu 30,000 Mutum 100
Dudu 20,000 Mutum 100
Kujerar Hajji Mutu 1

 

Ali Nuhu da Adam A Zango na daga Cikin Waɗanda suka yi Jawabin godiya ga Sanatan bisa Cika alkawarin da yayi musu, Inda sukai fatan Sauran Yan Siyasar Kasar nan zasu yi koyi da Sanata Barau Wajen tallafawa sana’ar su domin bunkasa ta tayi dai-dai dana Sauran masana’antu irin Kannywood.

 

Wannna tasa Yan masana’antar ta Kannywood maza da Mata suke ta Nuna godiya ga Sanatan Saboda abun da suka Kira da tallafin da masana’antar bazata manta da shi ba

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...