Gobarar Kurmi: Fa’izu Alfindiki ya jajantawa yan Kasuwar da gobar ta shafa tare da basu damar Gina shagunansu

Date:

Daga Maryam Khamis Diso
Shugaban karamar hukumar birni da kewaye, Kwamared Faizu Alfindiki, ya ziyarci kasuwar kurmi ‘yan littattafai da ke layin Alhaji Matazu, inda gobara ta tashi tare da konewar shaguna da dama sakamakon gobarar da ta tashi a daren jiya.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar yayin ziyarar jajantawa wadanda iftila’in gobarar ya afkawa, wasu daga cikin wayanda abun ya shafa sun bukaci shugaban da ya cire musu harajin da ake biya wajen yin sabon gini a kasuwar domin su mayar da ginin da sukai asara ba tare an biya ko kwabo ba.
Kwamared Faizu Alfindiki, ya ba su tabbacin cewa za su iya yin gini ba tare da biyan kudin ba, karamar hukumar ta yafe musu, sannan ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su yi hakuri, yana mai cewa gobarar jarrabawa ce daga Allah Madaukakin Sarki.
Ya kara da cewa shugabancinsa na duban yadda za a inganta kasuwannin da ke cikin birni da kewaye domin su ci gaba da tafiya dai-dai da zamani. “Muna rokon Allah ya sanya salama acikin zuciyar ku ya kuma kawar da afkuwar hakan anan gaba”. inji shi.
Cikin Wata sanarwa da Hukumar Kashe gobara ta Jihar Kano ta fita tace akalla shaguna 41 ne Suka gone a Kasuwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...