Buhari ya aiyana Ranar da za’a gudanar da Babban taron APC na Kasa

Date:

Daga Junaidu Saani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na Kasa a watan Fabrairun Shekara ta 2022.
 Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja a ranar Litinin.
 Taron ya kuma samu halartar shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni wanda kuma shine gwamnan jihar Yobe da kuma gwamna Badaru Abubakar na Jigawa.
 Atiku Bagudu, wanda bai bayyana takamaiman ranar da za a gudanar da babban taron a watan Fabrairu ba, ya ce an sauya Ranar taron ne saboda har yanzu jihohi hudu ba su kammala taronsu ba.
 Ya ce: “A jiya, 21 ga watan Nuwamba, kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, inda muka yiwa kwamitin rikon godiya bisa kokarin da suka yi wajen jagorantar jam’iyyar.  Mun kuma gode wa shugaban kasa da ya ba su goyon baya don cimma aikin da aka dora musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin 2026 da ya kai N1.368 tiriliyan

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar...

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...