Rashin tsaro: Akwai ‘yan Gudun Hijira Masu tarin yawa a Kano – Dr Zahra’u Umar

Date:

Daga Halima M Abubakar

Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban jama’a ta jihar Kano Dr Zahra’u Mohd Umar tace gwamnatin jihar kano tana aiki ba dare ba rana domin inganta tsaro a fadin jihar.
 Dr zahra’u Mohd ta bayyana hakan ne a wajen wani taron kasa kan yaki da ta’addanci tare da masu ruwa da tsaki da abokan hulda wanda aka gudanar a Abuja .
Cikin Wata sanarwa da Jami’ar hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Bahijja Malam Kabara ta aikowa Kadaura24 tace Kwamishiniyar ta bayyana cewa, biyo bayan rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassan kasar nan a kano akwai dimbin ‘yan gudun hijira.
 Ta ce gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dukufa wajen magance duk wani rikici tsakanin mutane domin samun zaman lafiya da ci gaban al’umma .
 Kwamishiniyar ta kara jaddada bukatar hada karfi da karfe wajen inganta rayuwar ‘yan gudun hijira musamman ta fannin inganta , ilimi da kuma Lafiyar su .
 Da ta juya ga mahalarta taron Dr zahra’u Mohd ta bukace su da su yi amfani da wannan taro ta hanyar da ta dace don samun ci gaba.
 Ta kuma yi addu’ar Allah ya kawo mana dauki kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, ta kuma yi kira ga musulmi da su yi addu’ar Allah ya karawa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa...

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...