Shan Paracetamol ba bisa ƙa’ida ba ya na lalata hanta- Likita

Date:

 

Wata fitacciyar likita, Esther Oke ta baiyana cewa shan ƙwayoyin maganin paracetamol ba bisa ƙa’ida ba babban haɗari ne ga lafiyar ɗan-adam.

Oke ta baiyana cewa ƴan Nijeriya da dama sun ɗauki tsawon shekaru su na shan paracetamol ba bisa ƙa’ida ba sakamakon jahilci.

Ta yi ƙarin bayani cewa irin waɗannan magungunan masu rage raɗaɗi na ɗauke da sinadari mai ƙarfi na paracetamol wanda ya ke lalata hantar ɗan-adam idan a na shan shi ba tare da ƙa’ida ba.

“Shan ƙwayoyi kamar guda 3 a maimakon 2 da wasu su ke yi ya saɓawa yadda ƙa’idar shan magani da duniya ta amince da ita.

“Bincike ya nuna cewa ƙwayoyi biyu na magani a ka yarda a sha kuma sau uku a ranar har zuwa kwanakin da likita ya rubuta,” ta yi gargaɗi.

Daily Nigeria ta rawaito Likitarb ta kuma bada shawarar cewa kada mutane su sha magunguna sai da sahalewar ƙwararren likita.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin 2026 da ya kai N1.368 tiriliyan

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar...

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...