Ku koyawa ƴaƴanku son Annabi da Sahabbansa – Alh. Faruk waru

Date:

Kwamittin mauludin Gidan marigayi Alh uba waru ya  gudanarda mauludin fiyayyen halitta annabi sallallahu Alaihi wasallam kamar yadda mihaifinsu yake gudanarwa a lokacin yana Raye.

Alhaji faruk uba  waru ya bukaci iyaye  dasu Kara Sanya soyayyar Annabi sallallahu Alaihi wasallam  a zukatan ƴaƴansu Wanda yin hakan zai tallafa wajan samun  Al’umma ta gari.
Yace iyaye basu da abun da zasu yiwa ƴaƴansu fiye da basu ilimin addini wanda zai sa su san martaba da darajar Annabi (S A W) da kuma koyi da halaye da ɗabi’unsa.
Shi ma  a nasa jawabin Alkali Halhalatul kuza’i Zakariyya ya bayyana cewa al’ummma jihar kano mutane ne masoya annabi S A W da kuma sahabbansa, inda yace hakance tasa suke gudanar da bikin tunawa  da ranar haihuwa fiyayyan halitta annabi Muhammad sallallahu Alaihi wasalam .
Ya buƙaci al’ummar jihar kano su mai da hankali wajen yin addu’ar samawa kano da Nigeria zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.
 Taron mauludin ya samu halarta   malamai da sha’airai daga fadin jihar nan wadanda suka hadarda sakataren majalisar shura na Tijjaniyya sheikh Barrister Habib Muhammad Dan Almajiri da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...