Ƴan sanda sun ceto mutum 47 daga wani gidan mari a Kano

Date:

Ƴan sanda sun ceto mutum 47 daga wani gidan mari a jihar Kano.

Gidan da ake bayyanawa da gidan gyaran hali wuri ne da iyaye kan tura ‘ya’yansu da ke muggan dabi’u da shaye-shaye da aikata manyan laifuka.

Lokacin da ‘yan sanda suka kai samame a ranar Alhamis, sun ceto mutum 47 duk maza da shekarunsu ke tsakanin 14 zuwa 35 sanye da sarkoki. Jikinsu duk dauke ya ke da alamar duka.

Kakakin ‘yan sanda Abdullahi Haruna ya shaidawa BBC cewa an cafke mutumin da ke da gidan mari kuma za a gabatar da shi a kotu.

Gwamnatin jihar dai ta haramta irin wadannan gidaje watanni 10 da suka gabata bayan kai sameme a ire-iren wadannan gidaje da ake cin zarafi ko azabtar da mutane da sunan tarbiyya.

‘Yan uwa da iyayen yara na cewa su na aike yaransu irin wadannan wurare ne saboda rashin cibiyoyin gwamnatin na gyara hali.

Mutanen da ake ceto yanzu haka na samun kulawa a asibiti.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...