A taron da aka kammala na inganta abichi a shekarar 2021 wanda aka gudanar a dakin taro na Ladi Kwali, dake otel din Sheraton, Abuja, mahalatta taron kamfanoni masu zaman kansu a masana’antun Aikin Gona sun amince su goyi bayan aiwatar da shirin Samar da Farfajiyar Aikin Gona ta farko da za’a gabatar a Kano dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
Kamfanin Silvex International wanda ke jagorantar aikin yana daga cikin mahimman masu ruwa da tsaki da suka halarci Babban taron inganta Abinchi a Najeriya na 2021 Mai taken Tsarin samar da Abinci Mai inganci don bunkasaTattalin Arzikin Kasa bayan cutar Covid-19.
Cikin sanarwar da Babban Jami’in Kamfanin Silvex International Limited Abubakar Garba Ibrahim ya aikowa Kadaura24 yace taron ya mayar da hankali kan bukatar yin amfani da ingantaccen makamashi a bangaren aikin gona a Najeriya don karfafa tattalin arzikin kasa bayan Covid-19.
Taron ya jawo hankalin manyan Jami’an gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu don karawa juna sani kan ingantattun ayyuka tsare -tsare na saka hannun jari da dabarun aiwatar da dabarun don rage tasirin cutar Covid-19 a Najeriya.
Sanarwar tace Bankin Ci gaban Afirka da sauran masu saka jari masu zaman kansu a yayin Babban taron Ciyar da Najeriya na 2021, Silvex International ta tallafa wa shirin Farfajiyar Kamfanonin Aikin Gona da aka shirya za a Samar a karamar hukumar Bunkure ta Kano wanda zai zama irinsa na farko a Najeriya.
Aikin yayin kammala shi, zai zama shagon tsayawa ɗaya ga duk masu ruwa da tsaki da ke aiki a cikin sarkar darajar tattalin arziƙi kuma yana da damar kirkirar dubban ayyuka kai tsaye.
Idan Zaku iya tuna gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ba da izinin kafa Farfajiyar masana’antun Aikin Gona a watan Yuni, 2021 a matsayin wani ɓangare na gudummawar jihar don samun wadataccen abinci a Najeriya.
Yayin da yake gabatar da Farfajiyar masana’antun Aikin Gona ga masu ruwa da tsaki, Manajan Darakta da Babban Darakta, Silvex International Limited Alh. Abubakar Usman Karfi ya ce zai gudanar da aikin ne da kansa. Don haka ya nemi tallafin saka hannun jari kan aikin daga kamfanoni masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan.
“Kano tana da fa’ida mai tarin yawa a matsayin babbar cibiyar tattarawa da kasuwancin manyan kayan aikin gona, wuri ne mai kyau na saka hannun jari tare da tsaro da aminci da ya haɗa abubuwan more rayuwa kamar wutar lantarki, hanyoyin mota, layin dogo, tashar jiragen ruwa don sauƙaƙa kasuwanci”. Abubakar Karfi ya nanata
A jawabinsa a wurin taron, Shugaban Bankin Raya Afirka Farfesa Akinwumi Adesina wanda babban mai ba shi shawara na musamman kan harkar masana’antu Farfesa Oyebanji Oyelaran-Adeyinka ya Wakilta yace ya amince ya hada hannu da duk masu ruwa da tsaki wajen tallafawa zuba jari ga bangaren Noma a Najeriya. .
Kamfanin Silvex International ya Sanya babban bankin yankin nan, tare da wasu masu saka jari dake zaman kans dillalan saka hannun jari da bankunan kasuwanci da su jawo hankalinsu don samar da Farfajiyar masana’antun Aikin Gona a Najeriya.
Farfesa Oyebanji ya kuma yi ishara kan bukatar yin aiki tare tsakanin Bankunan Agro-Processing Zones (SAPZ) na yanzu da bankin da ake ginawa na shirin Farfajiyar masana’antun Aikin Gona da ke Karamar Hukumar Bunkure ta jihar Kano.