Daga Abdullahi Kano
Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Nasiru Yusif Gawuna, wanda Kuma shi ne kwamishinan aikin gona yace gwamnatin jihar ta Samar da dabarun zamani domin inganta amfanin gona, tare da tabbatar da wadatuwar Abinchi a jihar Kano.
Dr Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da Rediyon Najeriya a Kano.
Ya ce Gwamnatin Gandujes tun da aka kafa ta, ta fara Canza tunanin Manoma ta yadda za su kasance masu himma da nufin cimma burin da aka sa a gaba.
Mataimakin Gwamnan ya bayana cewa Jihar kano ta samar da ingantaccen tsaro wanda ke haifar da kyakykyawan yanayi ga noma, Hanyoyi na zamani don jigilar kayan amfanin gona daga ƙauyuka zuwa birane domin sayarwa Cikin Sauki.
“Mun Horos da Manoma sabbin dabarun Aikin Gona na Zamani, mun samar da kayan aiki ga manoma musamman taki, tare da samar da ƙwararrun ma’aikatan da suke faɗakar da Manomanmu, Haka zalika mun samar da kwararrun malaman gona dubu guda Domin inganta Harkar wadata al’umma da Abinchi”.inji Gawuna
“Jihar Kano tana da manyan wuraren ban ruwa waɗanda muke ƙoƙarin gyara mafi yawansu, don ku ci gaba da wadatar da wadataccen abinci, dole ne mu iya yin noma aƙalla sau biyu a shekara don wadata al’umma da Abinchi”.
Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa a karkashin Shirin inganta aikin gona, Gwamnatin Jiha ta sami nasarori da dama da suka danganci Inganta Ayyukan Noma.
Ya yi kira ga Manoma da masu ruwa da tsaki da su yi amfani da kudaden da aka basu ta Hanyar data dace, yana mai cewa an samar da ingantaccen tsarin bibiyar manoman don ganin sun yi amfani da tallafin aikin gona Wanda gwamnati da kungiyoyin daba na gwamnati ba suka samar da manufar cimma burin da aka sa a gaba.
Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya roki manoma da su yabawa kokarin gwamnati wajen tabbatar da cewa sun biya basussukan da aka ba su a lokacin da ya dace, domin wasu su amfana da wannan bashi da suma suka samu.