Dakatar da Abduljabbar: Babbar kotun kano ta Amince da bukatar lauyan sa

Date:

Babbar kotun Kano ta amince da bukatar da lauyoyin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara suka gabatar mata kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.

Alkalin kotun, Mai shari’a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la’akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.

A zaman kotun na ranar Laraba, babbar kotun ta bukaci karamar kotun majistiren da ta yanke hukuncin na baya da kuma malamin su dakata da daukar kowanne mataki har sai ta kammala yanke hukunci.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya shaida wa BBC cewa a yanzu an tattara gaba daya an koma gaban babbar kotun ke nan, kuma za a saurari bukatar lauyoyin da malamin suka gabatar a ranar 27 ga watan Yulin nan da muke ciki.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin lauyoyin Sheikh Abduljabbar Kabara, sai dai sun ce ba za su ce komai ba sai nan gaba.

Ranar 4 ga watan Fabrairun da ya wuce ne majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa’azi a duk faɗin jihar, saboda furta kalaman tunkura al’umma.

A wancan lokacin gwamnatin ta shaida wa BBC cewa ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro game da kalaman da malamin ke furtawa, shi ya sa ta dauki wannan mataki.

Tun a wancan lokaci ne gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan wadannan zarge-zarge, amma har yanzu bai gabatar da rahotonsa ba.

Shi dai Malamin ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ba ta yi masa adalci ba wajen daukar matakin ba tare da an ji daga nasa bangaren ba.

Ya nemi a shirya masa zama da malaman dake ƙalubalantarsa domin ya kare duk abin da yake faɗi, buakatar da gwamnatin ta amince da ita, kafin daga bisani kotu ta haramta yin zaman kasa da awanni 48 kafin a gudanar da shi

54 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...