Sarkin Kano ya bada auren ‘yar Sarkin Bichi ga Dan Buhari

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bai wa Yusuf Buhari, ɗan Shugaba Buhari na Najeriya, auren ‘yar Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, ranar Lahadi.

Tawagar wakilai ta nema wa Yusuf auren Zarah Nasir Ado ne a hannun sarkin Kano, wanda yaya ne ga sarkin na Bichi.

Wakilan da suka yi wa ɗan shugaban ƙasar walicci ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu sun haɗa da Gwamnan JIgawa Badaru Abubakar, da Ministan Shari’a Abubakar Malami.

Sauran su ne Gwamnan Borno Babagana Zulum, da tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, da Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna.

Daga bisani tawagar ta je garin Bichi domin gaishe da Sarki kuma surukin Shugaba Buhari wato Nasiru Ado Bayero.

Kano

Wata majiya ta shaida wa BBC Hausa cewa tambayar auren kawai suka je yi, wanda kuma Sarkin Kano Aminu Ado ya ba su, saɓanin rahotannin da ke cewa ɗaura auren aka yi.

Wasu majiyoyi sun ce matasan biyu sun haɗu da juna ne a Ingila yayin da suke karatu a can.

Yusuf ne ɗan Aisha Buhari na uku da zai yi aure tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

104 COMMENTS

  1. Обязательный претендент на титул wbo в супертяжелом весе Александр Усик уверен, что они с чемпионом мира по версиям wba, wbo, ibo и ibf Энтони Джошуа устроят поединок, который навсегда останется в истории. Усик Джошуа смотреть онлайн Британский боксер-тяжеловес Энтони Джошуа оценил силу своего следующего соперника, украинца Александра Усика. По его мнению, бой получится сложным. Джошуа готовит себя к 12 раундам. При этом британец заявил, что

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...