Hajjin Bana: Maniyata a Kano sun fara karbar Kudinsu

Date:

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta fara dawowa da alhazan da suka yi niyyar gudanar da aikin Hajin shekarar 2021 kudadensu.

Da yake kaddamar da mika cakin kudin ga maniyyatan wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar, Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan hana zuwa aikin Hajjin bana da Hukumomin Masarautar Saudiyya suka yi

Danbatta ya yi nuni da cewa, bayan samun wannan bayani, Hukumar Aikin Hajji ta Kasa ta sanar da dukkan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha a hukumance.

Babban sakataren ya kara da cewa hukumar aikin hajji ta kasa ta gayyaci dukkan shugabannin hukumomin alhazai don ganawa da kuma mataki na gaba da ya kamata a dauka, wanda suka amince ba tare da wata tababa ba kan a biya maniyyatan kudadansu ko kuma a sanya su cikin shirin adashin gata ga wadanda suke da muradi

Sakataren zartarwar ya jaddada cewa sun fara aikin ne bayan samun izini daga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a wannan batun, inda yay kira ga maniyyatan da su tuntubi Jami’an alhazai na kananan hukumominsu ko kuma duk wani jami’i a Hedikwatar kan mayar musu da kudaden nasu.

Dambatta ya tunatar da cewa, tuni Hukumar ta kaddamar da kwamitin mutum goma sha biyar wanda ya kunshi duka masu ruwa da tsaki da suka hada da, wadanda suka hada da na ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, da na hukumar karbar korafi ta jaha da kuma wakilin kafafen yada labarai da sauransu

Tun da farko, Shugaban Hukumar, Farfesa Abdallah Saleh Pakistan, ya shawarci Mahajjata da su dauki hana zuwa hajjin a matsayin nufin Allah Madaukakin Sarki da kuma ci gaba da yin addua ba dare ba rana domin Allah Ya kawar da annobar COVID-19 tare da samun zaman lafiya a Kano, Najeriya da ma duniya baki daya.

A jawabansu daban-daban, wasu daga cikin Mahajjatan da suka karbi cakin kudinsu, yabawa shugabancin Hukumar Alhazai ta Kano suka yi kan yadda suka tsara yadda za a mayar da kudaden.

305 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Dalilin da ya hana Sarki Aminu Ado Bayero zuwa gidan yari na goron dutse a yau alhamis

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin...

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnatin jihar Kano ta ce a...

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

Daga Umar Ibrahim kyarana   Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar...