Rundunar Sojin Ruwa zata Gina Makaranta da Barikinta a kano

Date:

Daga Mubarak Bashir Jogana

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin bada duk Wata Gudunmawa domin Samun nasarar Samar da makarantar Sojin Ruwa a jihar Kano.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi alkawarin Yayin daya karbi bakuncin ayarin Rundunar da Suka zo Kano bisa Umarnin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Kasa Admiral Auwal Zubairu Gambo.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya Zama wajibi gwamnatin jihar Kano ta Yi abun daya dace don karuwar Makarantar sojin ruwan a Kano.

Yace Wannan Matakin da Shugaban Rundunar Sojin Ruwan ta Kasa ya nuna cewa jajjirtaccene Kuma Mai kishin cigaban Kano da Kasa baki daya.

Ganduje yace wanzuwar Sojin Ruwa a Kano Zai sa Matasan jihar su Rika sha’awar Aikin Sannan Kuma tsaron jihar Zai Kara inganta.

Gwamna Ganduje ya Samar da wani Kwamitin da Zai Sanya idanu domin tabbatuwar Aikin Makarantar da Kuma Asibiti Mai Gado 200 da Kungiyar Matan Jami’an Rundunar zasu Samar a Kano.

Gwamna Ganduje yace gwamnatinsa zata Samar da kyakkyawan yanayi ga Jami’an a lokacin da zasu gudanar da Babban taron su na Kasa Wanda zasu yi a nan Kano tare da bada tabbacin bada dama ga Shugaban Rundunar na Kasa Admiral Auwal Zubairu Gambo domin gabatar da makala a Daya Daga Cikin jami’o’in da ake dasu a Kano domin Kara cusa son Aikin Sojin Ruwa ga Matasan jihar nan.

Da yake nasa jawabin tun da fari Jagoran Ayarin da Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ya turo jihar Kano domin Fara domin duba filin da Gwamnatin Kano ta Baiwa Rundunar Admiral COR Ezekobe yace sun zo Kano ne domin tabbatar da alkawarin da aka kulla tsakanin gwamnatin Kano da Rundunar Sojin Ruwa lokacin da gwamnan ya Ziyarci Shugaban Rundunar a Abuja.

Admiral COR Ozekebo ya Kara da cewa Shugaban Rundunar Admiral Auwal Zubairu Gambo ya umarceshi daya Nemi izinin Gwamnan domin gudanar da Babban taron su na Kasa a Nan Kano.

Jagoran Ayarin ya Kuma yabawa Gwamna Ganduje bisa aiyukan Raya Kasa daya gudanar a Kano.

50 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...