Za Mu Samar Da Sabo Tsarin Bunkasa Masana’antu don Samin Karin Haraji – Shehu Na-allah Kura

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata samar da wasu sabbin tsare-tsare Wanda zasu kawo cigaba da bunkasar kanana da manyan masana’antu da nufin samar da Karin ayyukan yi da kuma Haraji.

Kwamishina Kudi na jihar Kano Muhammad Shehu Na-allah Kura ne ya bayyana hakan a ziyarar da wakilan hukumar raba tattalin arzikin kasa ta gwamnatin tarayya suka kawo kano tare da zagayawa domin duba kanana da manyan masana’antu da ake dasu.

Shehu Na-allah Kura ya ce makasudin ziyarar shine yadda hukumar zata tallafawa gwamnatin jihar Kano hanyoyin bunkasa samun kudin shiga domin rage dogara da kason da jihar Kano take samu daga gwamnatin tarayya.

Kwamishinan ya ce sun zagaya tare da duba ayyukan kamfanonin da suke samar da Bilo da masu yin fenti da kayan daki da kamfanonin sarrafa shinkafa da masu sarrafa Biscuit da Alawa harma dama masu sarrafa fatoci domin samar da wasu tsare-tsare wanda hakan zai basu damar daukar Karin ma’aikatan da Karin kudin shiga ga gwamnatin jihar Kano.

A jawabinsa shugaban ayarin Sunday Akon Anyang ya ce sun zo Kano ne domin tallafawa gwamnatin jihar Kano da nufin bunkasa samun kudin shiga domin rage dogaro da gwamnatin tarayya.

Sunday Akon Anyang wanda Hassan Nuhu Sambo yayi jawabi a madadinsa ya jaddada cewa gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kano za su cigaba da kokarin bunkasa hanyoyin samar da wutar lantarki wacce ita ce ta kasance babbar matsalar da kanana da manyan masa’antu ke fama da ita.

A nasa bangaren shugaban shugaban cibiyar kasuwanci ciniki da masana’antu ta kasa rashen jihar Kano Dalhatu Abubakar ya ce sama da kaso 90 cikin 100 na kasar noma a arewacin kasar nan ba’a amfani da ita sakamakon rashin samun tallafi daga gwamnatoci.

Wakilinmu Sani Magaji Garko ya rawaito mana cewa Dalhatu Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tallafawa manoma da masu kamfanoni irin su da kayan noma na zamani inda ya ce matukar hakan ta samu iya manoman arewacin kasar nan zasu iya ciyar da Nigeria baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...